Isa ga babban shafi

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta fara sanar da sakamakon zabe da aka gudanar

A jiya asabar ne hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta gudanar da zaben cike gurbi a wasu jihohin kasar 26 cikin 36.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

 

Yanzu haka dai an fara tattara sakamakon zabukan a jihohin da aka gudanar.

Jihohin da aka gudanar da zabukan sun hadar da Ebonyi da Yobe da Kebbi da Lagos da Ondo sai Taraba da Benue da Borno da kuma Kaduna da Plateau da Akwa Ibom da Anambra da Cross River.

Sauran sun hadar da da Delta da Enugu da Jigawa da Katsina sai Adamawa da Bauchi da Bayelsa da Kano da Nasarawa da Niger da Oyo da Sokoto da kuma Zamfara.

An gudanar da zaben ne a mazabu 575 cikin kananan hukumomi 80.

A sakamon da hukumar zaben ta sanar jami’iyyar APC ce ta lashe a jihohin Neja da Lagos da Oyo da Ondo sai Cross River da kuma Yobe.

Sai dai a jihar Bayelsa jam’iyyar APGA ta lashe zaben, yayin da jami’iyyar PDP ta lashe a jihohin Jigawa da Bauchi.

Akwai rahotanni dake nuni da cewa tun a jiya asabar hukumar zaben ta soke wasu zabukan a jihohin Kano da Enugu da Akwa-Ibom, sakamakon karya ka’idojin zabe.

Kazalika wata sanarwa da hukumar ta fitar da safiyar Lahadin nan ta tabbatar da dakatar da baturen zabe mai kula da santoriyar Jos ta arewa a jihar Plateau, sakamakon batan wasu takardun kada kuria.

Haka kuma jami’iyyar NNPP ce ta lashe kujerun ‘yan majalisar dokokin jihar biyu da aka yi a jiya sabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.