Isa ga babban shafi
RASHIN MITA

Najeriya ta zargi kamfanonin sayar da wuta da yi wa marasa mita aringizon naira biliyan 105

Najeriya – Gwamnatin Najeriya ta zargi kamfanonin dake sayar da wutar lantarki 11 a cikin kasar da karbar kudaden da suka wuce kima daga hannun mutane sama da miliyan 7 a cikin watanni 9 da suka gabata.

Turakun samar da wutar lantarki a Faransa
Turakun samar da wutar lantarki a Faransa © AFP - Daien Meyer
Talla

Hukumar dake kula da makamashi ta kasar tace kamfanonin sayar da wutar da ake kira Disco sun karbi wadannan kudade da suka kai naira biliyan 105 ne daga hannun mutanen da basu da mita, wadanda ake tsuga musu kudaden da suka wuce kima.

Alkaluman da gwamnati ta gabatar sun ce kamfanin Disco na Yola ya karbi irin wadannan kudade daga hannun mutane dubu 42 da 902 wanda ya kai naira miliyan 541, sai kuma Abuja Disco da ya karbi kusan naira biliyan 18 daga hannun mutane miliyan guda da dubu 823 da 218.

Shi kuwa kamfanin Disco na Benin ya yiwa masu hulda da shi dubu 754 da 849 irin wannan karin da ya kai naira biliyan 10 da rabi, sai Disco na Enugu da ya karbi karin kusan naira biliyan 12 daga hannun kwastomomin sa sama da miliyan guda.

Kamfanin Disco na Eko dake Lagos ya karbi irin wadannan kudaden na kari da suka kai naira biliyan 14 da miliyan 13 daga hannun mutane dubu 371 da 828, sai kuma Disco na Ibadan da ya karbi naira miliyan 333 daga hannun kwastomomin sa dubu 143 da 465.

Kamfanin Disco na Jos ya karbi kudin da ya kai naira biliyan 13 daga mutane sam ada miliyan guda da dubu 200, sai Disco Ikeja da ya karbi kusan naira biliyan 21 daga hannun kwastomomin sa dubu 934 da 438, sannan Disco na Kaduna wanda ya karbi naira biliyan guda damiliyan 140 daga hannun masu karbar wuta daga hannunsa ba tare da mita ba dubu 126 da 71.

Shi kuwa kamfanin Disco na Kano naira miliyan 196 na irin wadannan kudaden kari ya karba daga hannun kwastomonin sa dubu 71 da 120.

Hukumar dake kula da makamashin tace zata ci tarar wadannan kamfanoni naira biliyan 10 da miliyan 505 daga ribar da suka samu saboda zubawa masu sayar wutar ba tare da mita ba kudin da ya wuce kima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.