Isa ga babban shafi

Matsalar karancin abinci ta jefa ‘yan Najeriya kan tituna

Rayuwar ‘yan Najeriya da dama ta tabarbare matuka sakamakon tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya tilasta fita wajen neman abinci da kuma cin shinkafa mara kyau, wadda a da ake amfani da su wajen ciyar da kifi, wasu rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Afp na bayyana cewa wasu lokutan jama’a na gina ramukan tururuwa da kuma cin kwari.

Wata unguwa a wajen garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. 25 Yuni, 2020.
Wata unguwa a wajen garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. 25 Yuni, 2020. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Makwanni da dama mazauna garuruwa tsakiya da arewacin kasar sun fito kan tituna suna nuna bacin ransu.A makon da ya gabata, a Suleja, kusa da babban birnin tarayya Abuja, daruruwan masu zanga-zangar sun yi tattaki kan tituna dauke da aluna masu rubutu da ke cewa: “Yan Najeriya na shan wahala.

A garin Minna da ke arewa ta tsakiya na jihar Neja , masu zanga-zangar sun tare tituna da kuma birnin Kano , birni na biyu mafi yawan jama'a a Najeriya, inda mata suka yi tir da tsadar fulawa.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda matan Najeriya mazauna arewacin kasar ke tonon iri da tururuwa ke ajiyewa domin ciyar da 'ya'yansu.

Masu bincike na ginar ramukan tururuwa
Masu bincike na ginar ramukan tururuwa Axel Ducourneau

Tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da kuma kula da harkokin kudi, lamarin da ya sa farashin man fetur ya rubanya har sau uku da kuma tsadar rayuwa, inda Naira takardar kudin kasar darajarta ke ci gaba da faduswa a kan dala.

Alkaluma da ake da su yanzu kam na nuni cewa yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a hukumance ya kai kashi 28.92 cikin 100 a watan Disamba, matakin da ya kai mafi girma cikin shekaru uku.

Akalla kashi 63 cikin 100 na al’ummar Najeriya miliyan 220 na fama da matsanancin talauci, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

Kusan mutane milyan 27 ne ke fama da yunwa a yankin Sahel
Kusan mutane milyan 27 ne ke fama da yunwa a yankin Sahel © Getty Images/himarkley

‘Yan Najeriya da dama sun kasa morar abincin da ake kira “kayan alatu” kamar nama, kwai, madara da dankali.

Ministan noma na Najeriya Abubakar Kyari ya fadawa majalisar dokokin kasar a ranar litinin da ta gabata cewa ana fuskantar matsalar karancin abinci a kasar biyo bayan annobar cutar covid-19 da kuma ambaliyar ruwa.

kasuwar doya a Lafiya dake Jihar Nasarawa
kasuwar doya a Lafiya dake Jihar Nasarawa © The Guardian

Amma a cewar Malam Ya’u Tumfafi, manaja a kasuwar hatsi ta Dawanau, da ke wajen birnin Kano, matsalar ta ta’allaka ne a wasu wurare: “masu hannu da shuni sun fara sayar da hatsin da suke ajiyewa da yawa a rumbuna”.

Don magance rashin jin daɗi, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a fitar da kusan tan 102,000 na hatsi da za a sayarwa a kan farashi mai rawusa .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.