Isa ga babban shafi

Najeriya za ta zuba tallafi a bangaren noma don bunkasa samar da abinci

Gwamnatin Najeriya ta ce zata sayarwa manoman kasar taki da irin shuka da kuma magungunan feshi cikin rahusa, ta yadda manoman za su biya rabin kudin kayan da aka basu, a karkashin shirin inganta noman da ke da nufin fadada shi wajen noma hekta dubu 323 a cikin wannan shekara.

Wasu manoma kenan da ke duba gonarsu a wani yanki na tarayyar Najeriya.
Wasu manoma kenan da ke duba gonarsu a wani yanki na tarayyar Najeriya. © guardian
Talla

Ministan noma na Najeriya Abubakar Kyari ya ce wannan shiri zai kunshi hekta dubu 123 na alkama da dubu 150 na shinkafa da dubu 30 na masara da kuma dubu 20 na rogo. Muhammad Kabir Yusuf na dauke da rahoto a kai.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.