Isa ga babban shafi

Babbar kotun Najeriya ta sake dage zaman shari'ar Nnamdi Kanu

Wata babbar Kotu dake Abujan Najeriya ta tsayar da 19 ga watan Maris na shekarar nan domin ci gaba da sauraron shari’ar mai fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu da ake zargin sa da aikata laifukan ta’addanci, wanda lauyoyin sa ke neman ba da da beli.

Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. REUTERS - Afolabi Sotunde
Talla

Lauyan gwamnati Adegboyega Awomolo SAN ya ce wannan shari’a na zuwa ne sakamakon hukuncin kotun koli wadda ta ba da umarnin sake shari’ar da ake tuhumar Kanu da laifuffuka guda bakwai a ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2023.

Awomolo ya kara da cewa kotun ta kuma tabbatar da kudirin da ya gabatar mata a ranar 8 ga wata Afrilun shekarar 2022, da ke tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa Kanu.

Wadannan laifuffuka ne suka sa Kanu tserewa zuwa kasar Kenya don samun mafaka, kafin jami’an tsaro na DSS su ka tasa keyar shi zuwa Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.