'Yan sandan Finland sun saki jagoran Biafra sa'o'i bayan kama shi
Jami’an ‘yan sandan kasar Finland sun saki Simon Ekpa fitacccen dan awaren da ke fafutukar neman kafa kasar Biafra a Najeriya, sa’o’i bayan kama shi da suka yi tare da yi masa jerin tambayoyi.
Wallafawa ranar:
A dai ranar Alhamis din da ta gabata jami’an tsaron kasar ta Finland suka kai samame gidan Ekpa tare da cafke shi, wanda ya dade yana ikirarin goyon bayan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta.
A ranar 15 ga watan Fabrairu Jakadiyar Finland a Najeriya, Leena Pylvanainen, ta bayyana rashin jin dadinta kan umarnin da Simon Ekpa ya baiwa dimbin mabiyansa na su hana gudanar zabukan kasar da suke tafe.
Tun a wacccan lokaci ne kuma, Pylvanainen ya ce jami'an tsaro a kaarsa Finland suka fara tuntubar juna dangane da matakin da za su dauka kan Ekpa.
A halin da ake ciki dai, an saki Ekpa da yammacin ranar Alhamis bayan da ‘yan sanda suka kama shi isa zarginsa da aikata wani laifi da ba a bayyana ba a Finland.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu