Isa ga babban shafi

Boko Haram ta sace mata 'yan gudun hijira sama da 100 a Borno

Rahotanni daga jihar Barno da ke arewacin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu mata sama da 100 da suka shiga daji neman itace daga sansanin gudun hijira da ke a garin Ngala, hedkwatar karamar hukumar Gambarou na Jihar

Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Borno.
Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Borno. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kawo yanzu hukumomi ba su yi karin bayani kan lamarin ba, amma wani mazaunin garin Saleh Abbas da wasu majiyoyi tsaro sun tabbatar adadin mata sama 113.

Sai dai wata majiya daga sansanin ‘yan gudun hijirar ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda mayakan Boko Haram din suka yi wa matan akasarinsu 'yan mata su kimanin 319 kawanya kafin awon gaba da su.

“Yan ta’addan sun kewaye su ne a dajin Bula kunte da ke yammacin garin Ngala. Sun sallami tsoffi, amma sun arce da 'yan mata 319 hazikai da wasu samari"

Hukumomi dai na gargadi dangane da hadari da ke tattare da zuwa dazuka domin neman itace, to sai dai duba da halin kunci da masamman 'yan gudun hijara ke ciki ke tilasta musu shiga dazukan domin neman na abinci.

Ko latsa alamar sauti domin sauraren abin da Saleh Abbas mazaunin Gamboru Ngala ya shaidawa RFI Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.