Rundunar sojin Najeriya ta fara farautar wadanda ake zargi da daukar nauyin ta'addanci a kasar
Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta fitar da sunayen mutum 97 waɗanda ta ce tana nema ruwa-a-jallo kan zarginsu da ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra’ayi da kuma barazana ga tsaron kasar.
Wallafawa ranar:
Daga cikin wadanda ake nema Kudu Maso Gabashin Nijeriya akwai jagoran dayan reshen kungiyar IPOB Simon Ekpa.
Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta sanar da cewa tana neman mutum 97 ruwa-a-jallo kan zarginsu da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da kuma barazana ga tsaron kasar.
Manjo Janar Edward Buba wanda shi ne daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja.
Mutanen da ake nema sun kunshi ƴan ta’adda da kwamandojinsu daga Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Tsakiya da Kudu Maso Gabashin Nijeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu