Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Kanal Makiga kan dawowar hare-haren Boko Haram a jihar Borno

Wallafawa ranar:

A Najeriya rahotanni daga yankin arewa maso gabashin kasar sun nuna yadda mayakan Boko Haram suka koma kai hare-hare bayan lafawar da suka yi, lamarin da ke zuwa kwanaki kalilan bayan rahoton gwamnatin jihar Borno da ya bayyana kawo karshen kaso 95 na masu akidar kungiyar ta Boko Haram.

Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke a sassan jihar Borno ta Najeriya.
Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke a sassan jihar Borno ta Najeriya. AFP - HO
Talla

Hare-haren baya-bayan nan dai sun hada da na garin Dikwa da kuma Gamboroun-Ngala wanda ya kai ga sace mata fiye da 100 sai kuma kone gidajen 'yan gudun hijira.

Dangane da wannan batu ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro Kanal Muhammad Sani Makiga mai ritaya, ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.