Isa ga babban shafi

'Yan bindiga 14 sun mutu a wani rikici da ya barke tsakaninsu a Zamfara

A Najeriya wani fada da ya barke tsakanin bangarorin ‘yan bindiga 3 a jihar Zamfara ya kai ga mutuwar akalla 14 daga cikin batagarin wadanda ke kai hare-hare tare da sace mutane don neman fansa.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafin X ya bayyana cewa rikicin ya barke ne tsakanin tsagin ‘yan bindigar da ke kauyen Kaurar Zomo da ke yankin Kunchin Kalgo na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, yankin da ke ganin tsanantar hare-haren ‘yan bindigar baya garkuwa da mutane don neman fansa.

A cewar bayanan ‘yan bindigar 14 suka mutu a rikicin tsakanin bangarorin batagarin 3 ciki har da jagororinsu 2 da suka kunshi Kachallah Gwande da Kachallah Madagwal

Zagazola Makama masanin tsaro da ke bibiyar halin da yanayin tsaro ya ke a kasashen tafkin Chadi, ya ce tsagin ‘yan bindigar 3 ya kunshi guda karkashin jagorancin Alhaji Tsauni sai kuma yaran Kachallah Jafaru da kuma na Kachallah Gwandu.

A cewar Makama kamar yadda jaridun Najeriya suka wallafa, da misalin karfe 3:45 na yammacin jiya Alhamis ne fadan ya barke inda kuma nan take aka kashe ‘yan bindigar 12 baya ga jikkata wasu da dama wadanda yanzu haka ke karbar kulawa a cibiyar lafiya ta Munhaye.

A cewar rahotanni tun farko Yaran Gwande suka farmaki yaran Jafaru a Kaurar Zobo kauyen da ke karkashin ikon tsauni lamarin dfa ya kai ga zazzafan fadan tsakanin bangarorin 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.