Isa ga babban shafi

Dole ta sanya mu raba tallafin abinci ga jama'ar mu - Zulum

Najeriya – Gwamnan Jihar Borno dake Najeriya, Babagana Umara Zulum yace dole ke sa shi raba kayan abinci ga jama'ar jihar sa wadanda matsalar boko haram ta hana su walwala domin samar da yanayin da za'a samu dauwamammen zaman lafiya.

Zulum na raba kayan abinci a Gajiram
Zulum na raba kayan abinci a Gajiram © Borno state government
Talla

Zulum yace yayin da gwamnatin sa ta mayar da hankali a kan raba abincin ga mabukata marasa karfi, ana kuma samun ci gaba wajen a bangarorin inganta rayuwar jama'a da suka hada da kula da lafiya da ilimi da tsaro da kuma gina kayan more rayuwa.

Yadda mata ke layin karbar kayan abinci a Gajiram
Yadda mata ke layin karbar kayan abinci a Gajiram © Borno state government

Gwamnan yace kayan abincin da yake rabawa na taimakawa wajen ceto rayuwar jama'a wadanda wannan iftila'i na rashin tsaro ya yiwa illa.

Yayin da yake tsokaci ga manema labarai a Gajiram dake karamar hukumar Nganzai, Zulum ya bukaci samar da yanayin da zai dore wajen kula da lafiyar jama'a, maimakon tallafin da ake ba su lokaci zuwa lokaci.

Gwamnan ya yi watsi da zargin cewar tallafin na mayar da jama'a dogara da gwamnati gaba daya, yayin da ya yi nuni da ayyukan da gwamnatin sa ke yi wajen inganta bangaren noma.

Masu layin karbar tallafi a Gajiram
Masu layin karbar tallafi a Gajiram © Borno state government

Akalla iyalai dubu 25 suka suka samu irin wannan tallafin da ya kunshi kudi naira miliyan 25 da kuma kayan abincin da suka hada da buhuna shinkafa da masara da kuma atamfa.

Zulum ya kuma bayyana cewar jihar Borno ta karbi tallafin abincin da ya kai buhu dubu 15 na shinkafa daga hukumar dake raya yankin arewa maso gabas, kuma tuni aka raba su ga jama'a

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.