Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya sa al'ummar Bini gudun hijira a fadar gwamnatin Zamfara

Daruruwan mutanen da suka tsere daga kauyen Bini da ke yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, sun taru a fadar gwamnatin jihar da ke garin Gusau don neman gwamnati ta samar musu da tsaro.

Kofar shiga fadar gwamnatin jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Kofar shiga fadar gwamnatin jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. © Daily Trust
Talla

A jiya Lahadi ne mutanen wadanda yawancinsu mata da kananan yara ne, suka dauki matakin hakan bayan janye sojoji da aka yi daga garin.

Daya daga cikin mazauna garin Malam Umar Salisu, ya ce a baya akwai sojoji a garin nasu, sai dai 'yan bindiga sun kashe wasu daga cikinsu sannan a ranar Lahadi aka kwashe sauran da ke nan, don haka suka yanke shawarar kwasho dukkanin iyalansu zuwa fadar gwamnatin jihar don ta samar musu da tsaro.

A lokacin da kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Alhaji Wadatau Madawaki ke wa mutanen bayani a madadin gwamnan jihar, ya ce ‘yan bindigar sun kara matsa kaimi wajen kai hare-hare ne saboda matakin gwamnatin jihar na kin yin sulhu da su.

Matawaki ya ce gwamnati ta tsara shirin yadda za a maida mutanen garinsu tare da rakiyar jami’an tsaro.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a shiyar Arewa maso Yammacin Najeriya, inda hare-haren 'yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu dabunnai da muhallansu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.