Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar dakatar da safarar tumatur zuwa Lagos

Kungiyar dillalan tumatur ta Najeriya da ta dillalan kayan abinci da kuma ta shanu sun yi  barazanar shiga yajin aikin  kai kayan tumatur zuwa jihar Lagos. Kuma sun dauki wannan mataki ne saboda irin barnar da aka yi masu a kasuwar da suke hada hadar tumaturin ta Oke-Odo ta jihar.

Tumaturi a kasuwa cikin kwandunan roba
Tumaturi a kasuwa cikin kwandunan roba AFP
Talla

 A wannan barna da akayi masu a kasuwar an lalata fankon kwandunan robobi dubu 60 na tumarin.

Shugaban hadaddiyar kungiyar  dillalan ne Alhaji Ahmed Alaramma  ya bayyana wannan kudurin nasu a yayain da ya gudanar da jawabi gag a manema labaru a Zarian jihar Kadunan Najeriya a ranar lahadin da ta gabata.

Shugaban ya ci gaba da cewa mambobin kungiyar sama da 70 ne suka bayar da hayan kwandunan ga dillalan tumaturin a fadin kasar aka lalata dubu 60 daga cikia dai-dai lokacin da ake Shirin mayar da su Arewacin kasar domin daukar wani sabon kaya.

Ya  kuma kara da cewa ana amfani da kwandon na roba ne saboda sassauta matsalolin asara da ake samu ne a kwandunan kaba domin na roban yafi ba da kariya.

Don haka shugaban ya ci gaba da cewa za suyi duk mai yiwuwa wajen ganin sun yi maganin faruwar irin hakan a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.