Isa ga babban shafi

Sojin Nijar sun kama ƙasurgumin ɗan bindidan da ya addabi ƙauyukan Najeriya

Dakarun Jamhuriyar Nijar sun cafke ƙasurgumin jagoran ƴan bindigar nan daya addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeiriya, Kachallah Mai Daji a kusa da garin Ilela na kan iyakar Najeriya da Nijar.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Kachallah Mai Daji ya shiga hannun dakarun Jamhuriyar  Nijar ne a yayin da ya ke yukurin satar dabbobi a tsakanin iyakar Najeriya da Nijar.

Rahotanni sun ce ƙasurgumin ɗan bindigan ya fi aikata aika-aikar tasa ne a yankin Ilela, inda ya ke yin ta’addanci a ƙauyukan Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Ɗan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da sauran ƙauyukan da ke yankin.

Wani masanin tsaro, Zagazola Makama, wanda ƙwararre ne a fannin yaƙi da ta’addanci ya ce Kachallah Mai Daji ya shafe sama da shekaru 10 yana addabar al’ummomin yankin arewa maso gabashin Najeriya kafin ya sauya wuri.

Ya kara da cewa ya kashe mutane da dama, ya kuma ƙona ɗimbim ƙauyuka tare da sace mutane da yawa, baya ga harajin da ya yi ta ƙaƙaba wa ƙauyukaa tsawon shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.