Isa ga babban shafi

Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan ziyarar aiki Netherlands da Saudiyya

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta tabbatar da dawowar shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu daga bulaguro da ya yi, bayan kwashe kwanaki ana cece-kuce kan rashin sanin halin da yake ciki da kuma inda yake.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin taron tattalin arzikli a Sudiyya. 29/04/24
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin taron tattalin arzikli a Sudiyya. 29/04/24 © Bola Ahmed Tinubu X
Talla

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Ba’aji labarin shugaban ba, tun bayan kammala taron tattalin arziki a saudiyya.

Ƙarshen ziyarar

A watan da ya gabata ne shugaban ya bar Najeriya a wata ziyarar aiki zuwa ƙasashen Netherlands da Saudiya, ziyarar da ta ƙare hukumace ranar 29 ga watan Afrilu, amma bai koma gida ba, lamarin da ya sa ‘yan Najeriya yin tambayoyi.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin sauka daga jirgin saman fadar shugaban Najeriya. 20/06/23
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin sauka daga jirgin saman fadar shugaban Najeriya. 20/06/23 © Bola Ahmed Tinubu X

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale a wata sanarwa a ranar 22 ga watan Afrilu ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai fara ziyarar aiki a kasar Netherland sannan kuma zai halarci taron tattalin arzikin duniya a kasar Saudiyya.

Ngelale ya ce ziyarar da ya kai kasar Netherlands ta biyo bayan goron gayyatar da firaministan kasar ta Netherlands, Mark Rutte ya yi masa.

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu zai tattauna da firaministan kasar da wasu batutuwa da suka hada da taron kasuwanci da zuba jari tsakanin Najeriya da ƙasar Holland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.