Za a je zagaye na biyu a zaben Nijar
Sakamakon zaben Nijar ya nuna sai an je zagaye na biyu tsakanin Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou da babban mai adawa da shi Hama Amadou, saboda rashin samun wanda ya samu kuri'in da ake bukata domin lashe zaben a zagaye na farko.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Issoufou ne ya ja ragama a zagayen farko na zaben wanda aka gudanar a ranar 21 da 21 na wannan watan na Fabarairu.
Issoufou mai shekaru 63 ya samu kashi 48.41 cikin 100 a zagayen farko yayin da ya ke neman wa’adi na biyu domin ci gaba da zama akan karagar mulki.
Shi kuwa Hama Amadou, tsohon firaministan kasar wanda kuma aka tsare tun shekarar bara sakamakon zargin sa da safarar yara kanana, ya samu kashi 17.41 cikin 100 a zagayen farko yayin da zai sake karawa da Issoufou a cikin watan Maris mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu