Hukumomin Nijar sun musanta an kai hari kan jami'an agaji
Hukumomin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar, sun karyata jita jita dake nuna cewa ‘yan bidinga na kai hari kan ayarin motocin kungiyoyin agaji dake taimakawa ‘yan gudun hijira da abinci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Fugu Bukar Kantoman Diffa, ya ce a ko da yaushe suna tare da ’yan gudun hijira da kuma jami’an da ke basu agaji, dan haka basu da masaniya a kan labarin.
A cewar Bukar, hasalima tun a farkon fara gudanar da ayyukan agajin, ba’a taba samun wani abu da yayi kama da kaiwa motocin kungiyoyin agaji da ke taimakawa ‘yan gudun hijirar hari ba, dan haka babu kamshin gaskiya cikin labarin.
A halin yanzu kuma Kantoman ya ce, akwai isasshen abinci da aka tanada domin ‘yan gudun hijirar, wanda hakan yasa hatta matsalar karancin abinci ma bata fuskantar su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu