Isa ga babban shafi

Ambaliya ta kashe mutane 64 a jamhuriyar Nijar

Akalla mutane 64 suka mutu sanadiyyar amballiyar ruwan sama a Jamhuriyar Nijar tun bayan da aka soma ruwa a watan yuni na shekarar bana. Amballiyar ta sa mutane kusan  dubu 69.515  rasa muhallan su kamar dai yada hukumomin kasar suka sanar a jiya asabar.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar. © Tchadinfos.com
Talla

 A wannan sabon rahoto da hukumomin kasar suka fitar,akalla gidaje dubu 7.812 iftila’in ya shafa,ana da mabukata 69.515,mutane  32 suka rasa rayukan su bayan ruftawar gidajen da suke ciki,sai wasu 32 da ruwa suka yi awon gaba da su.

Iftila'in ambaliya
Iftila'in ambaliya © AP

Yanzu haka wasu yankunan kasar ta Nijar na kokarin ganin sun shawo kan cutar Cholera da ta bullu tun ranar 11 ga wannan watan  da muke cikin sa wacce ta kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 daga cikin mutane 419 da suka kamu da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.