Isa ga babban shafi
Nijar-Senegal

Mabaratan Nijar 580 sun isa gida bayan kwaso su daga Senegal

Daruruwan ‘yan  Jamhuriyar Nijar da ke  yawon bara a titunan birnin Dakar na kasar Senegal, wadanda aka bayyana halin da su ke ciki a wani shirin talabijin aka maida su kasarsu a daren Juma’a zuwa Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wakilinsa na cewa.

Jamhuriyyar Nijar ta fusata da rahotan gidajen talabijin din Senegal kan mabaratan 'yan asalin jamhuriyyar ta Nijar.
Jamhuriyyar Nijar ta fusata da rahotan gidajen talabijin din Senegal kan mabaratan 'yan asalin jamhuriyyar ta Nijar. © PBEAHUNYKGE/Reuters
Talla

Jirgin da ya kwaso mabaratan 580, wanda gwamnatin Nijar ce ta yi hayarsa ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Yamai da karfe 1 da minti 20 agogon Nijar da Najeriya.

Jim kadan bayan saukar mabaratan a Yamai, ministan cikin gidan Nijar, Hamadou Adamou Souley ya ce gwamnatin kasar sa ta dau wannan mataki ne duba da yadda barar da su ke yi, ya ke bata sunan Nijar a idon duniya.

A makon da ya wuce ne tashar talabijin din Senegal ta TFM ta yada irin zaman kaskancin da wadannan mabarata ‘yan kasar Nijar ke yi a babban birnin kasar Dakar, lamarin da ya harzuka mahukuntan Nijar dama daidaikun al'ummar kasar da ke kallon matakin a matsayin cin mutunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.