Isa ga babban shafi

Bazoum na ziyarar hutun shekara - shekara a Zinder

Al’umma a Zinder na dakon shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum wanda ke fara hutun na shekara-shekara wannan Asabar 13 ga watan Agusta.

Shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, 13/08/22.
Shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, 13/08/22. © Presidence du Niger
Talla

Bisa al’ada dai hukumomin soji da na farar hula da ma dandazon al’umma daga sassan daban-daban na jihar ne  ke tarbar shugaban kasar da mai dakinsa, tare da mika godiyarsu da kuma taya shi murna bisa namijin kokarin kan nasarori da aka samu a tsawon wannan shekarar.

Shugaban zai yi amfani da wannan lokaci da zai kasance a kauyen Tesker na makiya wajen tattaunawa da bangarori daban-daban domin sanin matsalolinsu na yau da kullum da kuma Nazari kan kalubalen kasar masamman halin tsaro na yankin sahel.

Shugaban kasar kwashe tsawon wannan shekarar ne wajen aiki tukuru tare da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje don kare Nijar da kuma ganawa da al'ummar cikin gida, matakin al’umma da dama suka yaba da shi.

Batun tsaro da hadin kan al’umma na daya daga cikin batutuwa da ya fi maida hankali a kansu, masamman ganin yadda yake kai wa ziyar yankuna da mayaka masu ikirarin jihadi ke kai hare-hare kamar yadda aka gani a Anzourou da kuma Banibangou a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.