Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Nijar ya kusa 200

Ambaliyar da zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa a Jamhuriyar Nijar, ta yi sanadiyar mutuwar mutane 192, gami da tagayyara wasu mutanen sama da 263,000, tare da lalata gidaje fiye da dubu 30,000.

Nijar na sahun kasashen Afrika da suka gamu da mummunar ambaliya a bana.
Nijar na sahun kasashen Afrika da suka gamu da mummunar ambaliya a bana. AP
Talla

Alkaluman da hukumar kare hakkin jama'a a kasar ta Nijar ta fitar a jiya Alhamis sun nuna cewar ambaliyar ruwan ta kuma lalata makarantu, da rumbunan ajiyar hatsi da kuma cibiyoyin kula da lafiya da dama.

Yankunan da abin ya fi shafa dai sun hada da Maradi da Zinder a yankin tsakiyar kasar, sai Dosso a kudu maso yamma da Tahoua a yammacin kasar.

A shekarar 2021, mutane 70 suka mutu, yayin da wasu akalla dubu 200,000 suka tagayyara, sakamakon ambaliyar da aka yi yayin saukar daminar ta bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.