Isa ga babban shafi

Adadin wadanda ambaliyar ruwa ta kashe a Jigawa ya karu zuwa mutum 108

Adadin wadanda suka mutu sakamakon jerin ambaliyar ruwa da aka yi ta yi a sassan jihar Jigawa tun daga watan Agusta ya kai 108.

Ambaliya ruwa ta yi mummumar barna a jihar Jigawa ta arewacin Najeriya.
Ambaliya ruwa ta yi mummumar barna a jihar Jigawa ta arewacin Najeriya. BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Tun da farko, rahotanni sun bayyana yadda mutane 98 suka mutu biyo bayan ambaliyar, wadda ‘yan sanda suka ce sun rasu ne sanadiyyar tsawa, rugujewar gine gine, a yayin da wasu kuma ruwa ne ya ci su.

A wannan Asabar, kakakin ‘yan sandan jihar Jigawar, Lawan Adam ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Muhammad Badaru ya dawo daga balaguron da ya yi zuwa kasashen waje a ranar Juma’a, bayan da ya shafe makwanni 3.

Gwamna ya sha caccaka a kan yadda ya zabi ya yi balaguro a lokacin da mutanen jiharsa ke tsakar wannan bala’in, da kuma yadda ya gaza ziyartar yankunan da ambaliyar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.