Isa ga babban shafi

Karin mutane sun mutu a ambaliyar ruwan Jigawa

Rahotanni sun ce an samu karin mutane fiye 29 da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa da ke Najeriya, yayin da ambaliyar ke ci gaba da mamaye yankuna a sassan jihar.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wani yanki na Jihar JIgawa dake makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wani yanki na Jihar JIgawa dake makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya. AP - Sani Maikatanga
Talla

Karin adadin ya sanya yawan wadanda da suka mutu jumilla a ambaliyar ruwan jihar ta Jigawa kaiwa mutane 92, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Lawal Shiisu ya tabbatar.

Yayin karin bayani, Shiisu ya ce an samu hasarar rayukan gwamman mutanen ne sakamakon dalilan da suka hada da nutsewa cikin ruwa, hatsarin kwale-kwale, da tsawa, da rushewar gine-gine, sakamakon yanayi na saukar mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwa dai na ci gaba da yin barna a sassan Jigawa inda ta mamaye filayen noma da kuma yankuna da dama na jihar.

A makon da ya gabata hukumar kula da hasashen yanayin saukar ruwan sama ta Najeriya NIHSA ta tabbatar da cewa jihar Jigawa ke kan gaba wajen fama da matsalar ambaliyar ruwa a fadin kasar.

Ta ce kananan hukumomi 16 na jihar ne lamarin ya shafa hukumar ta ce zuwa ranar 7 ga watan Satumba, sama da mutane 72 ne suka mutu tare da hasarar dukiya mai tarin yawa a sassan jihar ta Jigawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.