Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun sake kashe fararen hula a Nijar

Wani hari da ake kyautata zaton mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wasu manyan motoci uku da babur a yammacin Nijar kusa da kan iyaka da Mali, ya yi sanadin mutuwar mutane 11, kamar yadda wasu majiyoyi a kasar suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Lahadi.

Yankin Banobangou da ke Tillaberi a yammacin Jamhuriyar Nijar.
Yankin Banobangou da ke Tillaberi a yammacin Jamhuriyar Nijar. Photo : Sayouba Traoré/RFI
Talla

An kai harin ne a yankin da ya hada iyakoki uku tsakanin Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da ke fama da matsalar mayaka masu alaka da Al-Qaeda da kuma kungiyar IS.

Wani jami’in karamar hukumar a yankin Banibangou inda aka kai harin ya ce ‘yan ta’addan sun tare manyan motocin guda uku ne da safiyar ranar Asabar, inda suka kashe mutane 9, tare da kashe wasu mutanen biyu da ke kan babur.

Kafin harin na baya bayan nan dai, an samu raguwar farmakin da ‘yan bindiga ke kaiwa a Banibangou, wanda ke cikin yankin Tillaberi mai fama da matsalar tsaro a Nijar.

Tashin hankali ya sha rutsawa da fararen hula a fadan da ake yi tsakanin mayakan masu ikirarin Jihadi da jami’an tsaro.

A watan Nuwamban shekarar 2021, hukumomi sun ce akalla mayakan sa-kai 69 aka kashe a yankin Banibangou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.