Wani bam da aka dana a gefen hanya ya kashe mutane a Nijar
Wani bam da aka dana a gefen hanya ya kashe wasu mutane biyu tare da jikkata wani guda a kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa wadanda suka rasa rayukan nasu mata ne, wadanda suke wucewa da jakunan su ta kusa da inda aka dana bam din a kusa da garin Bosso da ke yankin Diffa.
Bosso da ke gabar tafkin Chadi, yanki ne da ake yawan fuskantar hare-haren 'yan ta’adda masu ikirarin jihadi, ciki har da mayakan Boko Haram da abokan hamayyarsu ‘yan ISWAP.
A watan da ya gabata, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka harbe manoma 11 a Diffa, kamar yadda wani jami’in yankin ya tabbatar.
Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da suke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Sahel, wadanda suka fara tayar da kayar baya a kasar Mali cikin shekarar 2012, daga bisani kuma suka fantsama zuwa makwaftan kasashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu