Masu juyin mulkin Nijar sun zargi Faransa da shirin amfani da karfi a kansu
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun zargi gwamnatin Faransa da yunkurin amfani da karfin tuwo da wajen mayar da hambararren shugaban kasar Bazoum Muhammed Kan karagar Mulki.
Wallafawa ranar:
Ta cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce akwai wasu sojojin wata kasar waje da ba su fito karara sun kama suna ba, wadanda suka ce sun rika jefa wa masu zanga-zangar goyon bayan sojojin barkonon tsohuwa a Lahadi.
Sojojin sun kuma zargi Faransa da hada kai da wasu yan Nijar din wajen kitsa yadda za’a yi amfani da karfin soja wajen afka musu.
Zanga-zangar ta ranar Lahadi dai ta juye zuwa tarzoma, inda ta yi sanadin jikkatar mutane 6 da yanzu haka ke kwance a Asibiti.
Wannan na zuwa ne bayan da Faransa ta yi barazanar cewa duk zanga-zangar goyon baya ko kuma adawa da sojojin kar ta kai kan kadarorinta, ko kuma ‘yan kasarta da ke zaune a Nijar, matukar ba haka ba kuma za su dandana kudarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu