Gasar musayar al'adu da harsuna tsakanin masoya tashar Radiyo Faransa
Wallafawa ranar:
Kunna - 09:49
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya mayar da hankali kan gasar da masoya tashar radiyon Faransa RFI da aka fi sani da ''Club RFI'' suka shirya a birnin Lagos na Najeriya, wadda ke da nufin musayar al'adu da yaruka tsakanin mabanbantan masu sauraron tashar.
Gasar wadda ita ce karon farko da aka taba gudanar da makamanciyarta na da nufin fadada fahimtar yaruka tsakanin al'ummomi, tare da bayar da kyautukan kara kwarin gwiwa ga wadanda suka yi nasara.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu