Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Idi dan Chadi kan harin sabon birni da ya kashe mutane 40
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:02
Yan ta’adda sun yiwa kimanin mutane 40 kisan gilla a yankin sabon birni na jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, harin da ke zuwa kwana guda bayan makamancinsa da kashe wasu sama da 20 al’amarin da ke ci gaba da tayar da hankulan jama’ar yankin. kan hakan Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Honorable Idi dan Chadi tsohon shugaban karamar hukumar ta sabon birni ga kuma yadda zantawarsu ta wakana.