Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Dr Aliyu Gambo kan ranar yaki da cutar HIV AIDS ta duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:25
YAU ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da cutar AIDS ta duniya, da zummar nazari da kuma fadakar da jama’a halin da ake ciki game da cutar. A wannan shekarar Majalisar ta bukaci samun daidaito ne wajen kawo karshen cutar nan da shekara ta 2030. Dangane da wannan rana, mun tattauna da Dr Aliyu Gambo, shugaban hukumar yaki da cutar a Najeriya, kuma ga tsokacin da yayi mana akai.