Daliban Najeriya sun gudanar da zanga-zanga saboda mallamai
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:20
A Najeriya kungiyar dalibai ta kasar ta gudanar da wata zanga-zanga don nuna fushin ta game da yajin aikin da kungiyar malamai ta kasar ASUU ta tsunduma, da nufin janyo hankalin gwamnati don ta biya wa Malaman bukatar su.
To sai dai duk da bayanin da ke cewa kungiyar daliban ta tattauna da ministan ilimi na kasar, amma da alama tattaunawar ba ta haifar da da mai ido ba.
Sanata Auwal Lawal Na dabo, shine shugaban kungiyar dalibai ta kasar rehsen jami’ar Bayero da ke Kano, yayin zantawar sa da Rukayya Abba Kabara ya ce zanga-zangar ta su zata dauki sabon salo nan ba da jimawa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu