Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Matan shugabannin Afirka na bukatar bada gudumawa don kawo zaman lafiya a Afirka

Wallafawa ranar:

Shugabannin Kungiyar kasashen Afirka ta AU sun gudanar da taron su na musamman a Malabo dake Equtorial Guinea wanda ya mayar da hankali akan karuwar ayyukan ta’addanci da kuma juyin mulki a nahiyar Afirka. Yunkurin taron na cimma matsaya akan kafa runduna ta musamman wadda zata rika taimakawa kasashen dake fama da tashin hankali ya samu rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Uwargidansa Aisha Buhari, a Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Uwargidansa Aisha Buhari, a Abuja. Liberty
Talla

Sai dai kungiyar matan shugabannin na Afirka ta gabatar da bukatar bada gudumawa wajen ganin an samu zaman lafiya a Afirka baki daya ta hannun shugabar ta Aisha Muhammadu Buhari ta Najeriya.

Bayan gabatar da mukalar ta gaban shugabannin, Bashir ibrahim Idris ya tattauna da mai taimaka mata Hon Mohammed Sani Zoro, kuma kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron tsokaci da ya mana akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.