Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Ahmad Muhammad dan gudun hijirar da ya juye zuwa dan kwallo
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:47
Ahmad Muhammad guda ne cikin matasan da rikicin Boko Haram ya raba da ahalinsa tun ya na da shekaru 14, yayinda wani ya dauke shi zuwa London, amma kuma suka rabu a tashar jiragen sama.Bayan ya shiga rayuwar kunci, gwamnati Birtaniya ta kula da shi, abinda ya sa ya yi karatu, ya kuma fara taimakawa irin mutanen da suka fuskanci rayuwar kunci a karkashin kamfanin sa na ‘You versus You‘, kuma yanzu haka ya taimaka mutane sama da 500. Ga dai tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.