Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Barista Huwaila Muhammad kan karuwar hukuncin kisa a duniya

Wallafawa ranar:

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta koka kan yadda ake samun karuwar zartas da hukuncin kisa a duniya, inda a bara kadai aka zartaswa  mutane 576 hukuncin. Rahoto da ƙungiyar ta fitar ta ce a ƙalla an kashe mutane 579 a ƙasashe 18 - lamarin da ya sa hakan ya ƙaru da kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2020.

Amnesty International ta koka kan yadda ake samun karuwar zartas da hukuncin kisa a duniya, inda a bara kadai aka zartaswa  mutane 576 hukuncin.
Amnesty International ta koka kan yadda ake samun karuwar zartas da hukuncin kisa a duniya, inda a bara kadai aka zartaswa mutane 576 hukuncin. Getty Images/Volkan Kurt
Talla

Iran ce kan gaba a wannan lamarin, inda ta yanke wa a ƙalla mutane 314 hukuncin kisa, idan aka kwatanta da 246 da aka yi a shekarar 2020, sai kuma Saudiyya wanda hukuncin kisa da ta yanke ya ninku zuwa 65.

To sai dai ga masana irin su Barista Huwaila Muhammad Ibrahim ta ce har yanzu gwamnatoci na jan kafa wajen zartas da hukuncin na kisa kan masu laifi, kamar yadda ta shaidawa Rukayya Abba Kabara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.