Kungiyoyin kwadago a Najeriya na ci gaba da barazanar tsayar da al’amurra chak a kasar ta hanyar rufe dukannin ma’aikatu da sauran bangarorin ayyukan yau da kullum kamar bankuna da filayen tashi da saukar jiragen sama, bayan zanga-zangar lumana da suka shirya gudanarwa a Makon gobe, duk a kokarin su na mara wa kungiyar malaman jami’a ta ASUU a yajin aikin da ta shafe tsawon watanni tana yi.
A tattaunawar da Rukayya Abba Kabara ta yi da kwamared Muhammad Zakariyya wani mai gwagwarmayar kare hakkin dan Adam a Najeriya ya ce wannan shine kadai matakin karshe da ya rage don matsa wa gwamnatin kasar lamba don yin abin da ya dace.
Ga dai tattaunawar ta su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu