Bakonmu a Yau
Sojojin Chadi sun tsawaita lokacin mika mulki ga fararen hula
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:58
Hukumomin Chadi sun tsawaita wa'adin mika mulki ga bangaren dimokuradiyya da shekaru biyu, tare da cewa shugaban soji na kasar, Mahamat Idriss Deby Itno zai iya tsayawa takara domin fafatawa a zaben, matakin da tuni kasashen duniya suka yi tur da shi.
Talla
An yanke shawarar ce a taron hadin-kan kasa wanda akasarin manyan ‘yan adawa suka kaurace masa.
A game da wannan al’amari, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattaunawa da Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, malami a sashen kimiyar siyasa da ke Jami’ar Bayero ta jihar Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu