Khadija Abdullahi-Iya kan yadda Mata suka sha kaye a zaben Najeriya na 2023
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:15
A Najeriya kashi 96 cikin 100 na matan da suka tsaya takara na kujeru daban-daban a zaben shekarar 2023 ba su kai labari ba. Kimanin mata dubu 1 da dari 553 ne suka tsaya takara a zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma majalisun tarayya da na jihohi da aka gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris na wannan shekara.
Kan haka ne Isma'il Karatu Abdullahi ya tattauna da Hajiya Khadija Abdullahi-Iya daya daga cikin wadannan mata,wadda ta tsaya takarar gwamna a jihar Neja a karkashin inuwar jam'iyyar APGA, in da ta bayyana dalilin da ya sa mata suka sha kaye a zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu