Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Abdu Misau kan rigakafin cutar mashako da ta kashe mutane 600 a Najeriya

Wallafawa ranar:

Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontier ta ce Najeriya na fuskantar matsalar cutar mashakon da ba’a taba ganin irinta ba, sakamakon samun mutane sama da dubu 17 da suka harbu da ita, wadda ta kashe akalla 600 daga cikin su. 

Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya.
Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya. © ET healthworld
Talla

Wannan ya sa hukumar lafiya ta duniya da takwararta ta UNICEF suka kaddamar da shirin yin allurar rigakafin cutar a jihohi 14 da suka hada da Katsina da Bauchi da Borno da Kaduna da Kano da Jigawa da kuma Lagos. 

MSF ta ce a jihar Kano kawai cutar ta kama mutane sama da 12,000, kuma kusan kashi 70 na marasa lafiyar da suka je asibitin ta na MSF basu karbi allurar rigakafin ba, abinda ke nuna matsalar rigakafin da ake fuskanta yankin. 

Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abdu Yusuf Misau na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.