Isa ga babban shafi

UNICEF ta yi gargadi kan cutar Mashako da ta kashe sama da yara 100 a Najeriya

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF yace a cikin kasa da watanni 7 cutar mashako ta Diphtheria ta yi sanadiyar mutuwar kananan yara 122 a tarayyar Najeriya. 

Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya.
Wasu ma'aikatan jinya kenan da ke bawa yaran da ke fama da cutar Diphtheria kulawa a wani asibiti da ke kudancin Najeriya. © ET healthworld
Talla

Shugabar sashen yada labarai na UNICEF a Najeriya Ms Safiya Akau, ta ce hukumar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta shawo kan annobar cutar dake mumunar shafar bangaren numfashi har ta kai ga yin kisa.  

Shugabar sashen yada labarai ta UNICEF a Najeriya Ms Safiya Akau, ta ce ya zuwa watan yulin da ya gabata, akalla mutane 3,850 ake zaton na dauke da cutar, sai dai bincike ya tabbatar da cewa mutane 1,387 ne suka harbu da ita, kuma kashi 71.5 na masu dauke da ita yara ne masu tsakanin shekaru 2 zuwa 14 da haihuwa. 

Shugabar ta ce jihohin Kano da Yobe da Katsina da Lagos da Sokoto da Zamfara da kuma babban birnin tarayya Abuja ke dauke da kashi 98 na wadanda suka harba da cutar a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.