Isa ga babban shafi

Faransa ta yi watsi da jita-jitar cewa za ta kafa sansanin sojinta a Najeriya

Faransa ta nesanta kanta da jita-jitar da ke bayyana yiwuwar shirye-shiryenta na kafa wani sansanin Sojinta a Najeriya, bayan ficewarta daga kasashen yankin Sahel sakamakon tsamin alaka.

Shugaban Faransa,  Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. © Sarah Meyssonnier / Reuters
Talla

Sanarwar da ofishin jakadancin Faransar a Najeriya ya fitar, ya musanta dukkanin zarge-zargen, wanda tun farko wasu fitattun ‘yan arewacin kasar suka faro kan cewar kasar na shirin bayar da matsuguni don girke sojojin kasashen yammaci ciki har da Amurka da Faransa, ko da ya ke kwanaki kalilan bayan yaduwar wannan zargi gwamnatin kasar a farkon makon ta musanta, yayinda kwana guda a tsakani Faransar da kanta ta nesanta kanta da wannan zargi.

A wani jawabi na musamman da ma’aiktar harkokin wajen ta Faransa ta gabatarwa al’ummar Najeriya don kwantar da hankali kan jita-jitar kakakin ma’aikatar Bertrand de Seissan ya ce babu wata tattaunawa tsakanin kasashen biyu kan shirin girke dakarun.

Farrakar da aka samu tsakanin Faransa da kasashen da ta yiwa mulkin mallaka na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso wanda ya kai ga janye dakarunta, ya sanya zargin yiwuwar kasar ta yammacin Turai ta iya girke dakarunta a Najeriyar musamman bayan kusancin baya-bayan nan tsakaninta da gwamnati mai ci karkashin Bola Ahmed Tinubu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.