Isa ga babban shafi

Faransa na goyon bayan ECOWAS wajen dawo da dimukaradiya a yammacin Afrika

Kasar Faransa za ta ci gaba da taimakawa kungiyar ECOWAS a kokarin da ta ke yi na dawo da dimukaradiya a wasu kasashen yankin da ke fama da matsalolin tsaro.

Ministar kula da harkokin kasashen wajen Faransa, Catherine Colona, tare da shugaban Najeriya da ke jagorantar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu.
Ministar kula da harkokin kasashen wajen Faransa, Catherine Colona, tare da shugaban Najeriya da ke jagorantar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu. © Nigerian Presidency
Talla

Ministar harkokin wajen kasar Catherine Colona ta bayyana haka a ziyarar da ta ke yi yanzu haka a Najeriya, inda ta ke ganawa da hukumomin kasar domin tattauna batutuwan hadin kai da kuma tsaron yankin.

Tuni Faransa ta dakatar da aikin samar da tsaron da dakarun ta ke yi a kasashen Mali da Burkina Faso wadanda ke fama da matsalar tsaro, kafin ta dauki irin wannan matakin a Jamhuriyar Nijar, kasa ta 3 da sojoji suka gudanar da juyin mulki.

Yunkurin mayar da mulki ga fararen hula a kasar Mali da Burkina Faso sun gamu da tazgaro, yayin da sojojin Nijar suka bijirewa umarnin ECOWAS na gaggauta mayar da mulki ga fararen hula, inda suke bukatar shekaru 3 a kan karagar mulki.

Tuni kungiyar ECOWAS ta kakabawa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, matakin da yayi matukar illa a kan talakawan kasar, yayin da ta ce tana ci gaba da nazari a kan daukar matakin soji.

Colonna bayan ganawa da takwaranta na Najeriya, Yusuf Tuggar a Abuja, ta ce sun tattauna batun goyan bayan ECOWAS wajen mayar da doka da oda a Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

“Ya dace muyi fiye da haka, kuma zamu kasance domin taimakawa kokarin ECOWAS. Babu dalilin da zai sa haka ya dore, ba tare da yiwa al’ummar da ke zuwa nan gaba illa ba”.

Sai dai ministar ba tayi karin haske a kan matakan da suke dauka na taimakawa kokarin na ECOWAS ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.