ECOWAS ta yi watsi da tayin mika mulki bayan shekaru 3 da sojojin Nijar suka yi
Kungiyar Raya Tattallin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta yi wasti da tayin wa'adin shekaru 3 na mika mulki ga farar hula da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta yi.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na kungiyar, Abdel-Fatau Musah ne ya sanar da haka a ganawarsa da wata kafar yada labarai ta kasa-da-kasa.
A ranar Asabar, shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da aniyar sojojin ta mika mulki ga farar hula a cikin shekaru 3 a wani jawabin da ya yi ga al'ummar kasar ta kafar talabijin, lamarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen kasar.
Tawagar ta hadu da firaminista Ali Lamine Zeine, wanda ya tarbe su a filin tashi da saukar jiragen sama, kana ya jagorance su zuwa fadar shugaban kasa.
Bayan ganawa da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, tawagar ta ECOWAS ta tattauna da hambararren shugaban kasar, Bazoum Mohamed wanda bayanai ke nuni da cewa yana cikin koshin lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu