Isa ga babban shafi

Shugaban mulkin sojin Nijar ya kalubalaci matakan ECOWAS

Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar, ya soki takunkumin da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta kakaba mata, yana mai cewa bai dace ba.

shugaban Mulkin sojin Nijar na jawabi bayan ganawar sa da ECOWAS.
shugaban Mulkin sojin Nijar na jawabi bayan ganawar sa da ECOWAS. © ORTN
Talla

Suhagaban Ya bayyana hakan ne a wani shiri da aka yada a gidan talabijin na kasar a daren ranar Asabar da ta gabata.

Tchiani ya kuma bukaci a maido da wutar lantarki da gwamnatin tarayyar Najeriya ta katse a wani bangare na takunkumin da aka kakaba wa sojin da suka yi juyin mulkin, Wanda aka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Bazoum Mohamed  lokacin da tawagar ECOWAS ta ziyarce shi a inda yake tsare
Bazoum Mohamed lokacin da tawagar ECOWAS ta ziyarce shi a inda yake tsare © Nigeria Presidency

Shugaban gwamnatin sojin ta Nijar ya baiyana haka ne bayan ganawar da ta gudana tsakanin su da tawagar kungiyar ECOWAS, karkashin jagoracin tsohon shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar mai ritaya.

Wasu daga cikin masu goyon bayan sojoji da suka yi juyin mulki a Nijar
Wasu daga cikin masu goyon bayan sojoji da suka yi juyin mulki a Nijar © AFP

Inda Tchani ya cigaba da cewa akwai marasa lafiya da ke cikin halin kaka-ni-kayi a asibitoci saboda rashin wutar, wasu kuma da dama suka rasa rayukansu, sannan al’amura da dama sun tsaya cik a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.