Sojojin Nijar na shirin fara tattaunawa da Rasha
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun sanar da shirinsu na fara tattaunawa da Rasha don samar da masalaha da kuma kawo karshen rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da suka yi.
Wallafawa ranar:
Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine ne ya bayyana hakan bayan ziyarar da ya kai kasar Chadi.
Wannan na zuwa ne bayan da Rasha da Amurka sun bukaci mahukuntan yankin su dauki matakin kawo karshen matsalolin da suka taso.
Wutar rikicin na kara zafi, tun bayan da kasashen duniya da kuma kungiyoyi ke kara matsa lamba kan sojoji da su mayar da mulki ga Mohamed Bazoum da suka kwata daga hannunsa.
A yanzu dai, ana jiran a ga irin matakin da za a cimma wajen taron manyan hafsoshin kasashen ECOWAS a birnin Accra da ke gudana a wannan Alhamis kan yiwuwar afka wa Jamhuriyar Nijar da yaki ko kuma akasin haka.
Tun bayan juyin mulkin, an ga irin yadda ‘yan kasar suka rika nuna goyon baya ga sojoji, tare da adawa kasancewar Faransa a kasar da kuma bukatar Rasha ta shiga cikin lamarinsu da kuma kai musu dauki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu