Isa ga babban shafi

Ƴan Nijar sun gudanar da zanga-zangar neman gaggauta ficewar dakarun Amurka

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan Lahadin a Jamhuriyar Nijar, don neman sojojin Amurka su gaggauta ficewa daga ƙasar da ke karkashin mulkin soja, dai dai lokacin ake ɗakon wata tawaga daga Washington cikin 'yan kwanaki masu zuwa domin shirya janyewar sojojin cikin tsari.

Wasu masu zanga-zangar neman dakarun Amurka su janye daga Nijar.13/04/24
Wasu masu zanga-zangar neman dakarun Amurka su janye daga Nijar.13/04/24 AFP - -
Talla

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula 24 da ke goyon bayan gwamnatin ƙasar tun bayan juyin mulkin bara ne suka kira zanga-zangar da aka yi a garin Agadez da ke arewacin Hamada, inda sansanin sojin Amurkan mafi girma a Afirka ya ke.

A ranar Juma'a ne Amurka ta amince da janye sojojinta fiye da 1,000 daga ƙasar ta Afirka inda Washington ta gina wani sansani da ta kashe dala miliyan 100 domin sarrafa jiragen yaki marasa matuka.

Masu zanga-zanagar na rike da allunan da ke dauke da sakonnin bukatar ficewar dakarun Amurka.

"Nan Agadez ne, ba Washington ba, sojojin Amurka za su koma gida”

Faransa

Wadannan ƙungiyoyi ƙarkashin jagorancin Issouf Emoud na M62, sune suka shirya zanga-zangar neman ficewar sojojin Faransa da suka tattara inasu a bara suka bar ƙasar.

A watan da ya gabata ne dai rundunar sojin Nijar ta sanar da warware yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin ƙasar da Amurka, wanda ta ce kasancewar sojojin Amurkan ya sabawa doka.

Amincewar Amurka

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell ya amince da janye sojojin a wata ganawa da ya yi da Firaministan Ali Mahaman Lamine Zeine a birnin Washington, kamar yadda jami'an Amurka suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP bisa sharadin sakaya sunansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.