Isa ga babban shafi

Nijar za ta baiwa Mali litar man dizel miliyan 150 don farfado da lantarkin kasar

Gwamnatin Sojin Nijar ta kulla wata yarjejeniya da makwabciyarta Mali wadda za ta bayar da damar shigarwa kasar ta yammacin Afrika da litar man dizel miliyan 150 don tayar da komadar tashar samar da lantarkin kasar da ke fuskantar koma baya.

Ali Mahamane Lamine Zeine Niger
Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine. AFP - -
Talla

Fadar gwamnatin Sojin Mali da kanta ta sanar da shirin karbar man na dizel lita miliyan 150 daga makwabciyarta Nijar, kasashen da dukkaninsu ke karkashin mulkin Soji suke kuma fuskantar tarin takunkumai.

Akalla mutane miliyan 11 da ke wakiltar kusan rabin al’ummar kasar ne ke cikin matsanancin duhu sakamakon katsewar lantarkin tun bayan juyin mulkin Sojin kasar ta Mali a 2020.

Mali wadda ke fuskantar kamfar man fetur da na dizel za ta yi amfani da damar man da Nijar za ta fara fitarwa don wadata jama’arta, dai dai lokacin da alaka tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da karfafa tun bayan mayar da su saniyar ware.

Kasashen na Mali da Nijar wadanda dukkaninsu ke karkashin mulkin Soji, sun hade kansu ne da makwabciyarsu Burkina Faso a kokarin magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da suka yi musu katutu.

Nijar na gab da fara cin kasuwar danyen manta inda ko a farkon makon nan ta karbi tsabar kudi dala miliyan 400 daga kamfanin makamashi na China a matsayin wani bangare na cinikin danyen man da za ta sayarwa kasar a watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.