Isa ga babban shafi

Ana sa ran isowar tawagar Amurka Jamhuriyar Nijar a makon gobe

A mako mai zuwa ne ake sa ran wata tawagar ƙasar Amurka ta isa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda za su tattauna da gwamnatin sojin ƙasar da ta yi watsi da yarjejeniyar soji da ke tsakanin kasashen biyu.

Sansanin sojin Amurka da ke birnin Yamai
Sansanin sojin Amurka da ke birnin Yamai © Franck Alexandre / RFI
Talla

Kafar talabijin din ƙasar ta ruwaito cewar, a cikin rahoton ziyarar da Firaministan Nijar Ali Mahamene Lamine Zeine ya kai Washington, ya bayyana cewa tawaga ta musamman daga Amurka za ta je kasar don tattauna batun alakar difulomasiya da soji da kuma tattalin arziki a tsakaninsu.

Amurka dai ta dakatar da bai wa jamhuriyar Nijar tallafi tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin shekarar bara.

A cikin watannin da suka gabata ne kuma gwamnatin sojin Nijar ta bukaci Amurka ta kwashe sojojinta sama da dubu daya da ke kasar, bayan da ta zarge ta da aje sojojin ba bisa ka’ida ba a cikin kasarta.

Ko a karshen watan da ya gabata, sai da daruruwan al’ummar Nijar suka yi zanga-zangar neman ficewar sojojin Amurka daga kasarsu. Irin matakin ne da suka dauka wajen ganin sojojin Faransa da ta yiwa ƙasar mulkin mallaka sun fice daga cikinta a karshen shekarar da ta gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.