Isa ga babban shafi

Sojin Nijar za su dandana kudarsu muddin wani abu ya samu Bazoum - EU

Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi sojojin da ke mulki a Nijar game da lafiyar hambararren shugaban kasar, Bazoum Mohamed wanda ake ci gaba da tsare shi tun bayan yi masa juyin mulki a watan jiya, tana mai cewa, lallai sojojin za su dandana kudarsu muddin wani abu ya same shi.

Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Shugaban Hukumar Gudanarwar EU Charles Michel a jawabinsa na wannan Juma'ar, ya gargadi cewa, sojojin na Nijar za su dandana kudarsu idan har suka bar lafiyar Bazoum ta shiga wani yanayi.

A baya-bayan nan ne sojojin na Nijar suka bai wa Bazoum damar ganin likitansa bayan bayanan da ke cewa lafiyarsa na cikin wani hali.

Charles Michel wanda ke wannan gargadi yayin zantawarsa da shugaban Najeriya kuma jagoran kungiyar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ta wayar tarho ya bayyana cewa wajibi ne sojojin su kula da lafiyar hambararren shugaban.

Kiran na Charles Michel na zuwa a daidai lokacin da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin ci gaba da kasancewa karkashin mulkin soja lura da yadda fararen hula ke cikin mawuyacin hali.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.