Isa ga babban shafi

ECOWAS ta musanta cewa ta kusa cimma matsaya da gwamnatin sojin Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta karyata labarin da ke cewa jagoranta, shugaba Tinubu ya ba da shawarar mika mulkin Nijar ga farar hula nan da watanni tara masu zuwa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka, bayan kammala taron ECOWAS a Abuja, ranar 10 ga watan Agusta, 2023.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka, bayan kammala taron ECOWAS a Abuja, ranar 10 ga watan Agusta, 2023. AP - Gbemiga Olamikan
Talla

A cikin sanarwar da kamfanin dillancin labarai na kasar ya samu daga hedkwatar hukumar ECOWAS da ke Abuja, ta ce kudurin mika mulki ga Nijar na bogi ne.

Martanin na ECOWAS ya zo ne bayan fitar da wani rahoto da ke bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya ba da shawarar mikawa farar hula mulkin Nijar daga nan zuwa watanni tara masu zuwa.

ECOWAS ta ci gaba da cewa tana kan bakarta kan juyin mulkin Nijar.

"Hukumomin soja a Nijar dole ne su maido da tsarin mulkin kasar nan take ta hanyar 'yantar da shugaban kasar Mohamed Bazoum," in ji ECOWAS.

Jawabin da aka danganta ga Tinubu a ranar Alhamis  ya ce a shekarar 1999 shugaban mulkin sojan Najeriya na wancan lokacin, Janar Abdulsalami Abubakar, ya mika mulki ga hukumomin farar hula kasa da shekara guda da hawansa mulki.

Ta haka ne Tinubu ya nemi gwamnatin mulkin Nijar karkashin jagorancin Abdourahamane Tchiani, da su yi koyi da irin matakin da Abubakar ya dauka a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.