Isa ga babban shafi

Najeriya na bukatar gina ban daki kusan miliyan hudu duk shekara-UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai bukatar Najerya ta gina ban-daki akalla miliyan 3 da dubu dari 9  duk shekara, don cimma burinta na kawo karshen bahaya a bainar jama’a da wasu mutane ke yi a kasar zuwa shekarar 2025 kamar yadda ta tsara. 

Najeriya na bukatar samar da ban daki kusan miliyan 4 a duk shekara-Open defecation: Nigeria needs 3.9 million toilets annually – UNICEF.
Najeriya na bukatar samar da ban daki kusan miliyan 4 a duk shekara-Open defecation: Nigeria needs 3.9 million toilets annually – UNICEF. Unicef
Talla

Shugabar sashen kulada ruwansha da tsaftace muhalli  na asusun, Dokta Jane Bevan ce ta bayyana haka a Litinin din nan a wajen bude bikin bude taron masu sana’ar gidajen bahaya a babban birnin kasar Abuja.

Bevan ta ce yanzu haka, sabbin wajen bahaya da ake ginawa a Najeriya duk shekara ya kama ne daga dubu dari da 80 zuwa dubu dari 2, tana mai cewa taron ya zo a lokacin da ake bukata, duba da cewa masu sana’ar gidan bahaya suna da gagarumar rawar da za su taka wajen kawo karshen kalubalen tsugunau a filin Allah ta’ala. 

Ta ce akwai bukatar sauya yadda aka saba yin abubuwa, ta wajen samar  wuraren biyan bukata, kuma bangare mai zaman kansa zai taka rawa wajen dorewa tare da karfafa sana’ar tsaftace muhalli a kasar. 

Ta ce sakamakon binciken bangaren da take jagoranta a UNICEF ya nuna cewa, mutane miliyan 48 ne ke bahaya a bainar jama’a  Najeriya, a yayin da  miliyan 95 suke rayuwa ba tare da mahimman ababen tsaftace muhalli ba. 

Ta ce Najeriya na asarar kashi daya da da digo 3 na kudaden shiganta ko kuma naira biliyan 455 duk shekara sakamakon rashin ingantattun hanyoyin tsaftace muhalli, inda ta ce wani abin da aka kashe a bangaren samar da ruwa da tsaftace muhalli, ana samun ribar da ke ribanya shi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.