Rayuwata kashi na 305 (Yadda wasu ke koyawa 'ya'yansu munanan dabi'u)
Wallafawa ranar:
Kunna - 09:59
Shirin namu ya mayar da hankali ne kan yadda wasu mazan ke kokarin bata tarbiyyar da iyaye mata suka gina ya’an su a kai, inda za ka iske suna koya musu wasu dabi’u da ke taimakawa wajen jefa su a wani hali, musamman yadda za su ke nuna musu goyon baya, ko da sun aikata laifi ne.
Lokuta da dama abokai sun fi kowa bada gudummawa wajen lalacewar tarbiyya, saboda yadda suke mayar da hankali wajen ganin wanda suke mu’amala dashi ya karbi dabi’unsu, to amma iyaye maza a yanzu ana ganin sun fi taimakawa wajen lalata tarbiyya yaran su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu